<span></span>
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin da take yi na ƙara kuɗin rajistar jarabawar kammala karatun sakandire ta WAEC da NECO da za a yi a baɗi.
Wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar safiyar wannan Litinin, ta ce an dakatar da shirin ne domin bai masu ruwa da tsaki dama su nazarci lamarin.
Sanarwar ta ce an janye wasiƙar da ma’aikatar ta fitar a ranar 18 ga Yunin 2026 wadda ke ɗauke da saƙon ƙara kuɗin jarrabawar.
A cewar ma’aikatar, an ɗauki matakin ne bayan ƙorafe-ƙorafe da shawarwarin da jama’a suka bayar kan shirin ƙarin kuɗin.
Ta bayyana cewa tun farko an yi tunanin ƙara kuɗin ne saboda hauhawar kuɗaɗen gudanar da ingantattun jarabawar ƙasa, inda ta ce kuɗin rajistar sun shafe shekaru ba tare da an yi musu kwaskwarima ba duk da ƙarin kuɗaɗen gudanarwa.
Ma’aikatar ta ce daga cikin abubuwan da suka haifar da buƙatar ƙarin kuɗin akwai kashe kuɗaɗen sufuri, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha, tabbatar da inganci da sauran muhimman ayyukan gudanarwa.
Sai dai Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ba da umarnin dakatar da shirin, yana mai jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen aiwatar da manufofi bisa tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gaskiya da kuma hujjoji.
Ma’aikatar ta ce dakatar da shirin na nuna aniyar gwamnati ta tabbatar da cewa duk wata manufa da za ta shafi miliyoyin ɗalibai da iyalansu sai ta samu cikakken nazari domin dacewa da muradun ƙasa.
Ta ƙara da cewa za a faɗaɗa tuntuɓe-tuntuɓe da shawarwari da hukumomin shirya jarabawa, ma’aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu da shugabanninsu, ƙungiyoyin iyaye, ƙungiyoyin ƙwadago, masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da sauran abokan hulɗa kafin a yanke hukunci na ƙarshe.
Ma’aikatar ta jaddada cewa ƙarin kuɗin rajistar jarabawar ba zai fara aiki ba har sai an kammala tuntuɓa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Ta kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa jin daɗin ɗalibai, tabbatar da samun ilimi mai inganci ga kowa da kuma aiwatar da manufofi cikin adalci na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanya a gaba a fannin ilimi.
A ƙarshe, ma’aikatar ta gode wa ’yan Najeriya bisa fahimta da goyon bayan da suke bayarwa, tare da alƙawarin ci gaba da sanar da jama’a yadda tattaunawar ke gudana.
