<span></span>
Ƙungiyar Hamas ta sanar da naɗa Khalil al-Hayya a matsayin sabon shugabanta, wanda ya gaji Yahya Sinwar da sojojin Isra’ila suka kashe a Zirin Gaza a watan Oktoban 2024.
Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa al-Hayya ya lashe zaɓen cikin gida bayan ya kayar da tsohon shugaban ɓangaren siyasar ƙungiyar, Khaled Meshaal, a zagaye na ƙarshe.
Al-Hayya, wanda a baya ya kasance mataimakin shugaban Hamas kuma ɗaya daga cikin mambobi biyar na kwamitin jagorancin ƙungiyar, ya ƙara samun tasiri bayan kashe Sinwar, kwamandan sojin Hamas Mohammed Deif a Gaza, da kuma Ismail Haniyeh, wanda aka kashe a lokacin wata ziyara da ya kai Tehran a shekarar 2024.
Bayan waɗannan asarori, al-Hayya ya kasance cikin mutum biyar da ke jagorantar kwamitin riƙon ƙwarya na Hamas, wanda aka kafa a ƙarshen shekarar 2024 domin gudanar da harkokin ƙungiyar a lokacin yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Al-Jazeera ta ruwaito cewa cewa shi ma al-Hayya ya tsallake rijiya da baya har sau biyu bayan yunƙurin kashe shi da sojojin Isra’ila suka yi a baya.
Naɗin Al-Hayya na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin Isra’ila da Hamas ke ci gaba da tsananta, inda ake sa ran zai jagoranci harkokin siyasa na ƙungiyar da kuma hulɗarta da ƙasashen waje.
Al-Hayya na daga cikin manyan jagororin Hamas da suka daɗe suna taka rawa a harkokin ƙungiyar.
Ya kasance ɗaya daga cikin masu wakiltar Hamas a tattaunawar tsagaita wuta da musayar fursunoni da Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani, musamman Masar da Qatar.
Shi ne ya jagoranci tawagar Hamas a tattaunawar tsagaita wuta da Isra’ila, wadda ta kai ga cimma yarjejeniya a watan Oktoban 2025. Sai dai yarjejeniyar ba ta kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila a Gaza ba.
