<span></span>
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta ce tana nazarin yiwuwar gudanar da gwajin zaɓen shugaban ƙasa kafin babban zaɓen 2027, domin tantance yadda tsarin gudanar da zaɓe da na’urorinta ke aiki.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da ya karɓi Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dakta Richard Montgomery.
Ya ce, an ɗauki wannan mataki ne sakamakon ƙorafe-ƙorafen da aka samu bayan zaɓen 2023, musamman kan amfani da fasahar zaɓe. Ya ce, hukumar na kuma duba yiwuwar yin cikakken bincike kan tsarin fasahar zaɓenta kafin zaɓen 2027.
A cewarsa, INEC za ta ci gaba da amfani da BVAS da kuma IReV, tare da ƙarfafa matakan tsaron intanet domin kare bayanan zaɓe da inganta amincewar jama’a da tsarin zaɓe.
Ya ƙara da cewa, gudanar da sahihin zaɓe ba aikin INEC kaɗai ba ne, sai da haɗin kan jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro da ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
