<span></span>
Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun ce sun kai wani hari da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan wuraren sojin Amurka guda 85 a ƙasashen Bahrain da Kuwait.
A wata sanarwa da IRGC ta fitar, ta ce hare-haren sun shafi sansanin Rundunar Sojin Ruwa ta Biyar ta Amurka da ke Bahrain da kuma sansanin jiragen sama na Ali Al-Salem da ke Kuwait.
Iran ta ce an kai harin ne domin mayar da martani ga abin da ta bayyana a matsayin hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan wasu muhimman cibiyoyinta a baya-bayan nan.
Rahotanni sun a bayan nan ne Iran ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani idan aka kai mata hari, lamarin da ya ƙara tayar da hankula kan yiwuwar rikicin ya bazu zuwa sauran ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Sai dai zuwa yanzu gwamnatin Amurka da hukumomin Bahrain ko Kuwait ba su fitar da wata sanarwa da ta tabbatar da iƙirarin Iran ko bayyana irin ɓarnar da aka samu ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa har yanzu ba a samu tabbaci mai hukumance kan adadin wuraren da Iran ta ce ta kai wa hari ko kuma ɓarnar da harin ya haddasa ba.
