<span></span>
Wata mahaukaciyar iska haɗi da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ta yi ɓarna mai yawa a wasu sassan birnin Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, inda aka yi ƙiyasin cewa ta yi ɓarna a gidaje sama da 3,500 har wasu sun rushe.
Lamarin dai ya raba iyalai da dama da matsugunansu bayan iska ta yaye rufin gidaje, shaguna, masallatai da sauran gine-gine.
Iskar, wadda aka yi a daren Asabar, ta fi shafar garuruwan Kwaimawa, Dan Masara, Rungumau da Takur Aduwa, inda mazauna yankunan ke ci gaba da ƙididdige asarar dukiyoyi ta miliyoyin naira.
Binciken da Aminiya ta gudanar bayan ziyartar wasu daga cikin yankunan da bala’in ya shafa ya nuna irin mummunar ɓarnar da iskar ta yi, inda wasu gidajen suka rushe gaba ɗaya ko wani ɓangare, rumfunan kasuwanni suka lalace, itatuwa suka tumɓuke, yayin da turaku da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki suka samu matsala.
Wasu sassan Otel ɗin Dutse Royal da ke yankin Takur Aduwa su ma sun lalace, yayin da gine-gine da dama a unguwannin da ke kewaye da yankin suka rasa rufinsu.
Mazauna yankunan sun bayyana cewa wannan na daga cikin mafi munin bala’in iska da suka gani a yankin cikin ’yan shekarun nan.
A Kwaimawa, ɗaya daga cikin yankunan da bala’in ya fi shafa, mazauna garin sun ce sama da gidaje 200 ne suka rushe ko wani ɓangarensu.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su kammala tantance yawan waɗanda bala’in ya shafa ba.
‘Kamar muna kallon fim ɗin bala’i’
Wani mazaunin Kwaimawa, Adamu Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa iskar ta zo da ƙarfin gaske da ya firgita jama’a, inda take yaye rufin gine-gine sannan ta rushe katangu.
“Mun fuskanci wata mummunar iska mai ƙarfi haɗi da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a wannan dare. A wannan gari kaɗai, sama da gidaje 200 ne suka lalace,” in ji Abdullahi.
Ya ce iskar ta kuma lalata wata tashar samar da ruwan sha mai amfani da hasken rana, wadda sama da mutum 3,000 ke amfana da ita, yayin da kayayyakin wutar lantarki da dubban mutane ke amfani da su suka samu matsala.
“Masallatai da dama sun lalace, ciki har da babban masallacin Juma’a namu, wanda iska ta yaye rufinsa,” in ji shi.
A cewarsa, motoci da dama sun lalace bayan rufin kwanuka da sauran tarkacen gine-gine suka riƙa faɗawa kansu.
Haka kuma, wasu kwantenoni da ake amfani da su a matsayin shaguna su ma iskar ta yi awon gaba da su.
“Itatuwa sun karye, dabbobi sun mutu, wasu sun ji raunuka, mutane da dama ma sun samu raunuka,” in ji wani mazaunin yankin.
Duk da girman ɓarnar, mazauna yankunan sun ba da tabbacin cewa ba a samu rahoton mutuwar wani mutum ba.
An ce wasu gidaje sun rushe a lokacin da mutane ke cikinsu, lamarin da ya sa maƙwabta da ’yan uwa suka shiga aikin ceto cikin gaggawa.
“A wasu wuraren, bayan iska ta yaye rufin gidaje, sai gine-ginen suka rushe alhali mutane na ciki. A wasu gidajen kuma, har yanzu ba a gano ind rufin kwanukansu suka faɗa ba,” in ji wani mazaunin yankin.
Dukiyar shekaru ta salwanta cikin mintuna
Bayan alƙaluman gidajen da aka ƙiyasta sun lalace, akwai labaran iyalai da suka ga dukiyar da suka kwashe shekaru suna tarawa ta salwanta cikin ’yan mintuna.
Rabiu Ya’u, wani mazaunin yankin, na daga cikin waɗanda suka yi asarar dukiyoyinsu.
A cewar mazauna yankin, gidansa, wanda aka ƙiyasta darajarsa ta kai miliyoyin naira kuma aka yi masa rufi na zamani tare da adon POP, iska ta yaye rufinsa gaba ɗaya a lokacin da shi da iyalansa ke ciki.
Ga wani mazaunin ƙetare mai suna Hussaini Muhammad Ahmed kuwa, ɓarnar ta zo da wani irin raɗaɗi.
An ce ya yi tafiya zuwa ƙasar waje domin neman abin dogaro, yana aikowa da kuɗi lokaci zuwa lokaci domin gina gidan iyalinsa.
Sai dai bayan iskar, an ce ginin ya lalace ƙwarai da gaske.
“Ya tafi ƙasar waje neman kuɗi, yana ta aikowa domin a gina masa gida. Amma yanzu kusan babu abin da ya rage na ginin,” in ji wani mazaunin yankin da ya san halin iyalin.
Wata da abin ya shafa, Kandiya Kwaimawa, an ce ta sayar da gonarta domin samun kuɗin gina gidan da take fatan za ta zauna tare da ’ya’yanta. Sai dai iskar ta lalata ginin.
Mazauna yankin sun ce ɓarnar ta yi muni matuƙa, ta yadda kusan babu wani ɓangare na ginin da ya rage da ya dace da zama.
Ladiyo Alhaji Abudu, wani ɗan kasuwar kayan ɗaki da ke sayar da gadaje, kujeru da sauran kayan gida, shi ma ya yi asara mai yawa bayan wani gini ya rushe kan hajarsa da aka ƙiyasta darajarta ta kai miliyoyin naira.
Shamsi Abdullahi ma na daga cikin waɗanda gidajensu suka lalace, inda aka ce kusan babu abin da ya rage da za a iya tsinta daga gidan.
Ɗaya daga cikin labaran da suka fi taɓa zuciya shi ne na Ashiru Abdulkarim da iyalinsa.
A bayyana cewa kwanan nan matarsa ta haihu kuma ta tafi zaman jego gidansu kamar yadda al’ada ta tanada.
Ana sa ran za ta dawo gida tare da jaririnta ne lokacin da mahaukaciyar iskar ta afka wa yankin, ta tarwatsa gidan mijin nata.
Ga Malam Baba kuwa, iskar ta kwashe kwantenar da yake amfani da ita wajen sana’a.
An ce da farko ya nemi kwantenar ya rasa bayan iska ta ɗauke ta. Daga baya aka gano ta cikin mummunan yanayi, inda aka ce ba ta da wani amfani sai dai a sayar da ita a matsayin kayan gwangwan.
Kabiru Haladu, wani mai sana’a a cikin kwantena, an ce yana cikin shagonsa yana yi wa kwastomomi cajin wayoyin hannu lokacin da iskar ta tuntsirar da shi da abin da ke ciki.
A yankunan da Aminiya ta ziyarta, an ga motoci da dama da suka lalace bayan rufin kwanukansu, katakai da sauran kayan gine-gine daga gidajen da ke kusa suka faɗa kansu.
Mazauna yankunan sun kwatanta abin da suka gani tamkar wurin da aka yi wani babban hatsari.
“Wallahi, wurin ya yi kamar an yi mummunan hatsari a ko’ina lokaci guda,” in ji wani mazaunin yankin.
Gwamnati ta yi alƙawarin tallafi
Da Aminiya ta tuntuɓi Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), ta ce za ta tantance girman barnar domin gano adadin iyalan da bala’in ya shafa da kuma irin tallafin da suke buƙata.
Daraktan Tsare-tsare na hukumar, Bala Muhammad Garingabas, ya ce hukumar ta riga ta ƙara kaimi wajen gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a ƙananan hukumomi tun bayan fara daminar bana.
Garingabas ya ce gangamin na da nufin faɗakar da jama’a game da bala’o’in da ke da alaƙa da sauyin yanayi tare da ƙarfafa al’umma su ɗauki matakan kariya.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ta tanadi kayayyakin agajin gaggawa domin tunkarar bala’o’in da ka iya afkuwa a lokacin damina.
A cewarsa, an kuma yi shirye-shiryen samar da kayayyakin gine-gine, ciki har da siminti da kwanukan rufi, domin taimaka wa iyalan da gidajensu suka lalace.
Ya ce za a raba kayayyakin ne ga waɗanda aka tantance bayan kammala bincike a yankunan da bala’in ya shafa.
Yayin da mazauna Kwaimawa, Dan Masara, Rungumau, Takur Aduwa da sauran yankunan da lamarin ya shafa ke ci gaba da kwashe tarkacen gine-gine, iyalai da dama na fuskantar ƙalubalen samun matsuguni na wucin gadi da kuma yadda za su sake gina rayuwarsu bayan gidajensu sun salwanta cikin dare guda.

