<span></span>
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta naɗa Daniel Ogunmodede a matsayin sabon kocinta gabanin fara kakar gasar NPFL ta 2026/2027.
Ƙungiyar ta bayyana naɗin nasa ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyarta da ke Kano, a ranar Asabar, inda Ogunmodede ya bayyana shirinsa na farfaɗo da ƙungiyar.
Kocin mai shekaru 46, wanda kuma mataimakin kocin tawagar Super Eagles ne, ya ce zai gina ƙungiyar har ta kai ga nasara a kaka mai zuwa.
Ogunmodede, wanda ya jagoranci Remo Stars ta lashe gasar Firimiyar Najeriya a kakar 2024/2025, ya ce Kano Pillars za ta fafata tare da ba da mamaki a dukkanin gasar da za ta buga.
Ya ce samun nasara shi ne babban burin ƙungiyar, kuma za su yi iya ƙoƙarinsu wajen fafatawa domin lashe duk wata gasa da za su shiga.
Kano Pillars ta fuskanci matsaloli a ’yan shekarun nan, ciki har da rikice-rikice da hukuncin hana ta buga wasu wasanni a gida.
Ogunmodede ya buƙaci magoya bayan ƙungiyar su kasance masu haƙuri, haɗin kai da kuma goyon bayan ƙungiyar domin dawo da martabarta.
Ya bayyana cewa yana son yin aiki tare da kowa tare da karɓar shawarwari daga masu ruwa da tsaki domin ci gaban ƙungiyar.
Haka kuma ya yi kira ga magoya baya su guji abubuwan da za su iya jawo wa ƙungiyar fuskantar hukunci.
Ana sa ran Ogunmodede zai fara aiki a ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
