<span></span>
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake alaƙanta wa da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), tare da mallaka wa Gwamnatin Tarayya.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce, ta yanke hukuncin bayan ta amince da buƙatar da Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gabatar.
Kotun ta ce Malami da sauran waɗanda abin ya shafa sun kasa tabbatar da cewa an sayi kadarorin ne da kuɗaɗen halak.
Kotun ta kuma yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da Malami da matarsa da ɗansa da kuma wasu kamfanonin da ake dangantawa da kadarorin suka shigar, inda ta ce ba su da gamsasshiyar hujja.
Tun da farko EFCC ta shigar da ƙarar tana neman a ƙwace kadarori 57 da darajarsu ta kai kimanin Naira biliyan 212.8, tana zargin cewa an mallake su ne haramtacciyar hanya.
A watan Janairu, kotun ta bayar da umarnin ƙwace kadarorin na wucin gadi tare da umartar duk mai iƙirarin mallakarsu ya bayyana a gaban kotu.
Kadarorin da abin ya shafa suna jihohin Abuja, Kano, Kaduna da Kebbi.
Sun haɗa da otal-otal, makarantu, jami’a, gidajen mai, manyan shaguna, gidaje, gonaki da sauran gine-gine.
A yayin shari’ar, Malami, ya ce an mallaki kadarorin ne bisa doka kuma EFCC ba za ta iya danganta su da wani laifi ba.
Ya ce hukumar ta dogara ne kan zargi maimakon gabatar da hujjoji masu inganci, kuma ra gaza alaƙanta kadarorin da wani laifi.
Sai dai EFCC ta dage cewa bincikenta ya nuna an sayi kadarorin ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya, kuma an yi saye su da sunayen wasu ‘yan uwa da kamfanonin Malami.
A hukuncinta, Mai shari’a Abdulmalik, ta ce muhimmin abin da kotun ta duba ba shi ne wanda ya mallaki kadarorin ba, sai dai kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin sun samu ne ta haramtacciyar hanya.
Ta ce waɗanda ake ƙara sun kasa kawar da zargin da ake yi kan yadda aka mallaki kadarorin, saboda haka ta bayar da umarnin ƙwace su gaba ɗaya tare da mallaka wa Gwamnatin Tarayya.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, mai magana da yawun Malami, Mohammed Bello Doka, ya ce tsohon ministan zai ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Barrista Abba Hikima, ya bayyana hukuncin a matsayin abin kunya ga wanda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Lauyan Tarayya.
Ya ce lamarin ya nuna muhimmancin riƙon amana da gaskiya a jami’an gwamnati, sannan ya buƙaci gwamnati ta tabbatar an yi amfani da kadarorin da aka ƙwace wajen amfanar da al’ummar Najeriya.
Sannan ha nemi a mayar da jami’ar da ke cikin kadarorin zuwa cibiyar da za ta amfani jama’a.
