<span></span>
Tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), Farfesa Ango Abdullahi, ya ce Arewa na fuskantar manyan ƙalubale ne saboda ta yi watsi da kyawawan ɗabi’u da manufofin shugabannin da suka assasa yankin.
Ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna.
A cewarsa, Arewa ta rasa muhimman ɗabi’u kamar gaskiya, ladabi, sadaukarwa da shugabanci na gaskiya, waɗanda a da su ne ginshiƙan ci gaban yankin.
Ya ce, “An rasa kyawawan ɗabi’un Arewa. Da a ce mun riƙe ɗabi’un da iyayenmu da shugabannin farko suka bar mana, da Arewa ba ta tsinci kanta a halin da take ciki a yau ba.”
Farfesa Ango Abdullahi, ya buƙaci shugabannin Arewa na yanzu su yi koyi da marigayi Janar Hassan Usman Katsina, wanda ya bayyana a matsayin mutum mai gaskiya, riƙon amana da sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima.
A nasa jawabin, Dakta Jibrin Ibrahim Bugaje, ya ce Arewa ta shafe shekaru tana fama da taɓarɓarewar tattalin arziƙi, rashin tsaro, talauci da kuma raunin cibiyoyin gwamnati sakamakon gazawar shugabanci.
Ya ƙara da cewa rashin tsaro ya yi mummunan tasiri ga noma, kasuwanci da rayuwar al’umma.
Bugaje, ya kuma soki wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a Arewa da ke yawan ƙorafin matsalolin yankin ba tare da gabatar da mafita ba.
Ya tuna yadda marigayi Janar Hassan Usman Katsina, ya ƙarfafa masa gwiwa ya ci gaba da rubuce-rubucensa da ke kare gaskiya duk da suka da ya fuskanta daga wasu jami’an ƙasashen waje.
Ya ce shugabannin zamanin Janar Hassan Usman Katsina sun haɗa ilimin zamani da kyawawan ɗabi’u irin su ladabi, adalci da sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima.
An shirya taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina ne, domin girmama gudummawar da ya bayar tare da tattauna batutuwan shugabanci, mulki na gari da makomar Arewacin Najeriya.
