<span></span>
A ƙasar Mali, wasu mayaka masu ikirarin jihadi sun sake kai wasu jerrin hare-hare a yau asabar a wasu da dama daga gidajen yari da ke Gao, Anefis, Aguelhok da Sevare, da kuma wani gidan yari a Kenieroba .
Masu ikirarin jihadi dauke da manyan makamai tare da hadin gwiwar Abzinawa sun afkawa gidajen yari da nufin fitar da wasu daga cikin mutanen su da ake tsare da su a ƙasar ta Mali.
Rahotani na bayyana cewa,an ji karar harbe-harbe a yankunan a Gao,Anefis, Aguelhok da Sevare, da kuma wani gidan yari a Kenieroba.
Mohamed Elmaouloud Ramadane, mai magana da yawun Abzinawa,a wata sanarwa da ya fitar,ya na mai cewa mayakansu na cikin birnin” na Anefis.
A Gao, a arewacin Mali, sheidu sun tabbatar da harbe-harbe da “fashe-fashe a harabar bariqin sojoji.
A tsakiyar garin Sevare, an gwabza faɗa daga misalin karfe 5:00.
Rahotani na baya-baya na nuni cewa wasu maharan sun kai hari gidan yarin Kenieroba, inda ake tsare da wasu mayaka masu ikirarin jihadi, mai nisan kilomita 12 daga babban birnin Bamako.
