<span></span>
Manchester City ta sanar da ɗaukar matashin ɗan wasan gefe na Ingila, Jeremy Monga, daga Leicester City kan kwantiragin shekara biyar.
Monga mai shekara 17 ya koma City ne yayin da ya ke ci gaba da jan hankalin manyan ƙungiyoyi da dama, bayan da ya kafa tarihi a Leicester a matsayin ɗaya daga cikin mafi ƙarancin shekaru da suka buga wa ƙungiyar wasa.
Ko da yake ba a bayyana kuɗin cinikin ba, rahotanni sun ce yarjejeniyar ta kai fam miliyan 10, tare da wasu ƙarin tsarabe-tsaraben kuɗaɗe da kwantiragin ya tanada, wanda za a riƙa biya har zuwa shekarar 2031.
Monga ya buga wa Leicester wasanni 37, sannan ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya fara wasa a sahun farko na ƙungiyar.
Shi ne ɗan wasan Ingila na uku da Manchester City ta saya a kasuwar musayar ’yan wasa ta bana, bayan mai tsaron raga Pierce Charles da Elliot Anderson, wanda ya zama ɗan wasa mafi tsada da ƙungiyar ta saya a tarihinta.
Monga ya fara buga gasar Firimiya ne yana da shekara 15, lokacin da ya fito a matsayin canji a wasan da Leicester ta sha kashi a hannun Newcastle a watan Afrilun 2025 ƙarƙashin Ruud van Nistelrooy.
Ya kuma fara wasa a matsayin ɗan wasa na farko a gasar League Cup da Huddersfield a watan Agustan 2025.
Matashin, wanda ke taka leda a tawagar ’yan ƙasa da shekara 19 ta Ingila, shi ne ɗan wasa na uku mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa bugawa a Gasar Firimiya, bayan Ethan Nwaneri da Max Dowman.
Da yake magana bayan kammala cinikin, Monga ya ce bai yi wata-wata ba da ya ji Manchester City na son ɗaukarsa.
“Da na ji Manchester City na sha’awar ɗaukata, nan take na san wannan ne matakin da ya dace da ni.
“Burin kowane matashin ɗan wasa ne ya kasance cikin irin wannan babbar ƙungiya. Manchester City ita ce mafi ƙwazo a Ingila cikin shekaru goma da suka gabata.
“Ƙungiyar ta kuma bai wa matasa irin su Phil Foden da Nico O’Reilly damar fitowa, abin da ke nuna cewa akwai makoma mai kyau ga ’yan makarantar ƙungiyar.
“Babban abin alfahari ne a gare ni kasancewa a nan, kuma ina farin cikin komawa Manchester City,” in ji shi.
