<span></span>
Mai bai wa Shugaban Najeriya Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Manufofin Sadarwa, Daniel Bwala ya ce ba duk ’yan Najeriya da suka yi ƙaura zuwa Birtaniya neman ingantacciyar rayuwa ne suka samu abin da suke fata ba.
Da yake magana a shirin Morayo Show, Bwala ya ce da dama daga cikinsu, har da masu digirin farko da na biyu, na aiki ne a cibiyoyin kula da marasa lafiya da tsofaffi, lamarin da ya bayyana a matsayin “bauta ta zamani.”
A cewarsa, duk da matsalar rashin aikin yi da ake fama da ita a Najeriya, wasu masu karɓar albashin Naira 60,000 a ƙasar na iya kasancewa cikin yanayi mafi alheri fiye da wasu da suka yi ƙaura zuwa Birtaniya.
Ya ce, hakan na da nasaba da sauƙin samun taimakon iyali, damar samun rance da kuma ƙarancin tsadar rayuwa idan aka kwatanta da Birtaniya, inda ya ce tsadar rayuwa ke hana mutane cimma wasu daga cikin burinsu na kuɗi duk da samun ingantattun ayyukan more rayuwa.
