<span></span>
Matasa da ɗalibai a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, sun gudanar da zanga-zanga kan matsalar rashin tsaro, inda suka nemi Gwamnatin Tarayya ta ceto ɗaliban da aka sace a yankunan Mussa da Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba.
Masu zanga-zangar sun ɗauki alluna ɗauke da saƙonnin kira da a kawo ƙarshen ta’addanci da sauran laifuka.
Sun buƙaci ’yan Najeriya su haɗa kai wajen tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar.
Jagoran zanga-zangar, Suleiman Muhammed, ya yaba wa jami’an tsaro kan ceton ɗalibai da malamai da aka sace a Jihar Oyo.
Amma ya buƙaci gwamnati ta yi irin wannan ƙoƙari wajen ceto ɗaliban Borno da har yanzu suke hannun ’yan ta’adda.
Masu zanga-zangar sun kuma buƙaci gwamnati ta samar da ayyukan yi, horas da matasa sana’o’i da tallafa musu domin rage yawan shiga harkokin laifuka.
Sun yi gargaɗin cewa biyan ’yan ta’adda kuɗin fansa na iya ƙara ƙarfafa waɗannan hare-hare.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Muhammed Mustapha, ya ce ya kamata gwamnati ta yi bayani kan dalilin da ya sa aka fi mayar da hankali kan wasu ɗaliban da aka sace yayin da waɗanda ke Borno har yanzu ba a yi komai a kansu ba.
Ya kuma buƙaci a samar wa jami’an tsaro kayan aikin da suka dace domin yaƙi da ta’addanci.
