<span></span>
Mataimakiyar Shugaban Ƙasar Zambia, Mutale Nalumango, ta tsallake rijiya da baya tare da wasu mutum bakwai bayan jirgin sama mai saukar ungulu da suke ciki ya yi hatsari jim kaɗan bayan tashinsa a ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne yayin da Nalumango da tawagarta ke gudanar da yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar a ranar 13 ga watan Agusta.
Nalumango mai shekara 71 ta shaida wa gidan talabijin na Diamond TV cewa hatsarin ya afku ne bayan sun bar wani gangamin yaƙin neman zaɓe a garin Nakonde da ke arewa maso gabashin ƙasar.
“Bayan jirgin ya tashi, ban yi tsammanin ya wuce minti ɗaya ko biyu ba, sai kawai muka dawo ƙasa,” in ji ta, tana mai tabbatar da cewa ba ta samu wani rauni ba.
Ta ƙara da cewa, “Mu takwas ne a cikin jirgin, kuma dukanmu muna cikin ƙoshin lafiya.”
Har yanzu ba a bayyana musabbabin hatsarin ba, sai dai ta ce jirgin ya lalace matuƙa.
A cikin wata sanarwa, gwamnatin Zambia ta ce an duba lafiyar mataimakiyar shugaban ƙasar bayan hatsarin, kuma har an sallame ta daga asibiti bayan an tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna jirgin mai saukar ungulun na rundunar sojin saman Zambia kwance a gefe, bayan da ake zargin ya faɗa kan wani itace.
