<span></span>
Wasu matasa biyu sun ɓace bayan da ruwa ya kwashe su a wani kogi da ke unguwar Hayin Malam Bello a Jihar Kaduna, sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi da yammacin ranar Asabar.
Rahotanni sun ce matasan na kan hanyarsu ta dawowa daga Yammacin Kabala, lokacin da suka yi ƙoƙarin ƙetare kogin.
A lokacin, ruwan kogin ya ƙaru sosai saboda ruwan saman da aka yi.
Wani mazaunin yankin ya ce an gargaɗi matasan da kada su shiga kogin saboda hatsarin da ke tattare da hakan, amma suka ƙi ji.
Daga nan ne ruwa ya kwashe su.
Tun daga lokacin, mazauna yankin tare da jami’an ceto ke ci gaba da neman su, amma har yanzu ba a gano inda suke ba.
Shugaban al’ummar yankin, Alhaji Ibrahim Fage, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa lamarin ya jefa al’umma cikin baƙin ciki.
Ya kuma buƙaci jama’a, musamman matasa, da su guji ƙetare koguna a lokacin damina saboda ruwa kan ƙaru sakamakon ruwan sama.
A halin yanzu, jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kaduna na ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
Shugabar Ayyuka ta NEMA a Kaduna, Hajiya Halima Daudu Sulaiman, ta ce an fara aikin neman su da misalin karfe 11 na safiyar ranar Lahadi.
Ta jami’an hukumar za su ci gaba da aikin har sai an gano matasan.
