<span></span>
Hukumar Tsaro ta Jihar Kaduna (KADVS), ta kama wani mutum da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da ƙaramar bindiga.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Yunusa Shehu Ibrahim, ya fitar, ya ce Kwamandan KADVS, Ali D. Audu (mai ritaya), ya bayyana cewa wanda aka kama mai suna Samson Ayuba, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Sanarwar ta ce jami’an KADVS sun kama wanda ake zargin ne, yayin sintiri na yau da kullum.
Bayan bincike, sun gano bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, ƙaramar bindiga ƙirar gida guda ɗaya, wayar salula da wasu kuɗaɗe a hannunsa.
An miƙa wanda ake zargin tare da kayayyakin da aka ƙwato ga rundunar Operation Fushin Kada domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace.
Kwamandan KADVS, ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen yaƙi da masu aikata laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar Kaduna.
Haka kuma, ya buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai don taimakawa wajen yaƙi da miyagun laifuka.
