<span></span>
Jagoran Ɗariƙar Qadiriyya a Najeriya, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kan irin ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa, tare da buƙatar ya ƙara kaimi wajen ci gaba da aiwatar da su.
Shehin malamin ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata ganawa da Gwamnatin Kano ta bayyana a matsayin ta farko a hukumance tsakaninsa da gwamnan, wadda aka gudanar a Abuja.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ambato Sheikh Qaribullah yana taya gwamnan murnar nasarorin da gwamnatinsa ta samu, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, shiriya da kuma ci gaba da samun nasara wajen gudanar da mulki.
Jagoran Qadiriyyar ya kuma buƙaci gwamnan da ya ci gaba da ruɓanya ayyukan ci gaba, musamman a fannonin samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman sassa.
Haka kuma, ya tabbatar wa gwamnan cewa mabiya Ɗariƙar Qadiriyya za su ci gaba da yi masa addu’o’i da kuma bai wa gwamnatinsa goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa jagoran addinin bisa ziyarar, wadda ya bayyana a matsayin alama ta kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin gwamnatinsa da shugabannin addinai.
Ya kuma roƙi mabiya Ɗariƙar Qadiriyya da sauran ƙungiyoyin Musulunci da su ci gaba da yi wa jihar da ƙasa addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa, bunƙasar tattalin arziki da haɗin kan ƙasa, yana mai jaddada cewa addu’o’in malamai da al’umma na da matuƙar muhimmanci ga nasarar kowace gwamnati.
Gwamnan ya kuma sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi jin daɗin al’umma da kuma ɗorewa kan ayyukan ci gaba a faɗin Jihar Kano.
