<span></span>
Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kai hari Makarantar Sakandiren Gwamnati da ke Opada-Olowa a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi, inda suka sace shugaban makarantar, da jami’in kula da jarabawar NECO da wasu ɗalibai.
Rahotanni daga al’ummar yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Talata, lokacin da ɗaliban ke rubuta jarabawar kammala sakandire NECO.
An ce maharan, waɗanda ke ɗauke da muggan makamai, sun afka garin ba zato ba tsammani suna ta harbe-harbe a iska, lamarin da ya sa mazauna yankin suka watse domin tsira da rayukansu kafin su nufi makarantar.
Wani jagoran al’umma a yankin, Sunday Alkali, ya ce da farko maharan sun yi mamakin ganin mutane da dama na hutawa a ƙarƙashin bishiyoyi, abin da ya sa suka ja da baya na ɗan lokaci.
“Amma bayan wani ɗan lokaci sai suka dawo suna ta harbe-harbe, lamarin da ya sa jama’a guduwa domin tsira da rayukansu,” in ji shi.
Mazauna yankin sun ce bayan lafawar harbe-harben ne suka tarar da cewa maharan sun kai hari makarantar.
“Da muka isa makarantar, mun tarar da takardun jarabawa a warwatse a azuzuwa da harabar makarantar. Ba mu ga ɗalibai ko malamai ba.
“Daga baya muka tabbatar cewa sun sace shugaban makarantar, Mista Nyada Daniel, jami’in kula da jarabawar NECO, Mista Solomon Audu, da kuma ɗalibai mata biyu,” in ji wani mazaunin yankin.
Rahotanni sun nuna cewa ɗaliban da aka sace ba su da yawa saboda a lokacin da maharan suka kai harin, ɗalibai ƙalilalan ne kawai ke rubuta jarabawar Adabin Turanci (Literature in English) ba manyan darussa kamar Turanci da Lissafi ba.
An kuma ce zuwa yammacin ranar Talata, maharan sun fara kiran iyalan wasu daga cikin waɗanda suka sace, suna neman kuɗin fansa mai yawa domin sakin su.
A cewar Sunday Alkali, maharan sun tuntuɓi aƙalla iyalan mutum huɗu daga cikin waɗanda suka sace suna neman a biya su kuɗin fansa cikin gaggawa.
Sai dai jami’an soji da ’yan sanda, tare da masu sintiri da mafarauta, sun bazama cikin daji domin ceto waɗanda aka sace.
“Wannan lokacin da nake magana da kai, sojoji da ’yan sanda sun shiga sintiri a cikin daji suna bibiyar sahun maharan domin ceto waɗanda aka sace,” in ji wani mazaunin yankin.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta ce maharan sun sace ɗalibai huɗu, shugaban makarantar da kuma wani jami’in wucin gadi na NECO.
A cewarta, wata tawagar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ta ƙaddamar da aikin ceto nan take kuma tana ci gaba da bibiyar maharan.
Ta ƙara da cewa an riga an ceto ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda aka yi garkuwa da su da kama waɗanda suka aikata laifin.
Har ila yau, ta bayyana cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, CP Naziru Bello Kankarofi, da Kwamandan Soji na yankin, da Mai Bai Wa Gwamnan Kogi Shawara Kan Tsaro, sun nufi wurin da lamarin ya faru domin tantance halin da ake ciki.
Ta yi alƙawarin cewa rundunar za ta fitar da cikakkiyar sanarwa da zarar ta samu ƙarin bayanan da aka tabbatar da ingancinsu.
Lamarin na zuwa ne bayan wani harin da aka kai a yankin makonni kaɗan da suka gabata, inda aka kashe wani manomi a gonarsa, abin da ya sa al’ummar yankin suka umarci makiyaya da su fice daga yankin.
