<span></span>
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar ƙasa biyu da ta afku a Venezuela a watan jiya ya haura 5,000, yayin da gwamnati ta sanar da samun kuɗaɗen tallafi daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF) domin ayyukan sake gina yankunan da bala’in ya shafa.
A cewar Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar, Jorge Rodriguez, adadin mamatan ya kai 5,069, inda mafi yawan asarar rayukan ta auku a Jihar La Guaira da ke arewacin birnin Caracas, wadda girgizar ta fi yi wa ɓarna.
Sai dai adadin waɗanda suka jikkata bai sauya ba, domin har yanzu ya tsaya a 16,740, yayin da aka ce yawancinsu sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.
A wata sanarwa kuma, shugabar riƙon ƙwarya ta ƙasar, Delcy Rodriguez, ta ce Venezuela ta samu dala miliyan 346 daga IMF domin tallafa wa ayyukan farfaɗo da yankunan da bala’in ya shafa.
Babbar Daraktar IMF, Kristalina Georgieva, ta tabbatar da sakin kuɗaɗen, tana mai cewa an bai wa Venezuela damar amfani da wani ɓangare na kuɗaɗenta da ke ajiyar asusun domin biyan buƙatun gaggawa na jin-ƙai.
Har yanzu kusan mutane 20,000 da bala’in ya raba da muhallansu na ci gaba da rayuwa a sansanonin wucin gadi, inda ake fama da ƙarancin ruwan sha da kuma rashin ingantattun hanyoyin tsaftar muhalli.
Tun farkon wannan shekara ne IMF da Bankin Duniya suka dawo da hulɗa da Venezuela bayan shekaru ana dakatar da ita, lamarin da ya bai wa ƙasar damar sake amfani da wasu daga cikin kuɗaɗenta da ke ajiye a cibiyoyin kuɗi na duniya.
