<span></span>
Aƙalla mutane kusan dubu uku ne suka mutu sakamakon mummunar girgizar ƙasa har kashi biyu da suka afku a Venezuela kamar yadda sabbin alƙaluman gwamnati suka nuna a ranar Asabar.
Sabbin alƙaluman sun nuna cewa mutum 2,954 sun riga mu gidan gaskiya a yayin da ƙungiyoyin ceto na ƙasa da ƙasa suka fara kawo ƙarshen ayyukan neman waɗanda suka tsira.
Adadin mamatan ya ƙaru da sama da mutum 300 idan aka kwatanta da na ranar Juma’a, bayan girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.2 da 7.5 da ta afku ranar 24 ga Yuni, wadda ta bar dubban mutane babu matsuguni.
A yayin da sama da mutum 16,500 suka jikkata, har yanzu ana ci gaba da neman dubban mutane da suka ɓace. Sai dai duk da cewa gwamnatin Venezuela ba ta fitar da ƙididdiga ba, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa mutum kusan 50,000 ba a san inda suke ba bayan girgizar.
Bayanai sun ce Lardin La Guaira, da ke arewacin babban birnin ƙasar, Caracas, shi ne ya fi fuskantar ɓarna, inda gidaje da dama suka rushe.
Hukumomi sun ba da labarin cewa bayan afkuwar girgizar ƙasar, an sake samun motsin kasa har sau 942 a yankin.
Kwana goma bayan aukuwar girgizar, ƙungiyoyin ceto sun fara dakatar da aikin neman waɗanda suka tsira, yayin da iyalai ke ci gaba da neman gawarwakin ’yan uwansu a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.
Shugabar riƙon ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez wadda ta ce al’ummar ƙasar na cikin tsananin alhini, ta karrama ƙungiyoyin ceto na ƙasa da ƙasa da lambobin yabo, ciki har da karnukan da suka taimaka wajen aikin ceto.
Ƙungiyoyin ceto daga Amurka da wasu ƙasashen Kudancin Amurka sun sanar da fara tattara kayansu domin komawa gida, bayan binciken da suka gudanar bai nuna alamar akwai sauran masu rai a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen ba.
Sai dai wasu ’yan Venezuela sun nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira jinkirin martanin gwamnati, suna cewa iyalai ne suka fara tono ’yan uwansu kafin isowar masu aikin ceto.
Rodríguez ta kare matakan da gwamnati ta ɗauka, tana mai cewa an tura dubban jami’an tsaro da masu aikin agaji domin gudanar da ayyukan ceto.
