<span></span>
Wani bene mai hawa biyu da ake ginawa a titin Sultan Road da ke Jihar Kano ya rufta da safiyar Juma’a, inda mutum huɗu suka maƙale a ciki baraguzai.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9 na safe.
An samu nasarar ceto mutum uku daga cikin waɗanda suka maƙale, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto mutum na huɗu.
Shaidu sun ce ma’aikatan da ke aikin ginin sun lura da alamun matsala a ginin yayin da suke aiki, lamarin da ya sa suka yi saurin ficewa daga wajen.
Sai dai mutane huɗu, ciki har da wani jami’in tsaro da mai direban Adaidaita Sahu, sun maƙale sakamakon rushewar ginin.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan ginin, Shuaibu Yaro, ya shaida wa Aminiya cewa suna ɗaukar siminti zuwa saman ginin ne lokacin da injiniyan wajen ya lura da alamun cewa ginin zai iya ruftawa.
Ya ce ma’aikatan sun yi saurin sauka, amma wasu mutanen da ke kusa da ƙofar ginin sun maƙale bayan ginin ya rufta.
Yaro, ya ƙara da cewa an ceto mutane uku, ciki har da jami’in tsaron da wani abokinsa, kuma an kai su Asibitin Sir Muhammadu Sanusi da ke Kano domin samun kulawar likitoci.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ana ci gaba da ƙoƙarin ceto mutumin da ya maƙale a cikin ginin.
