<span></span>
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ziyarci Sanata Rufa’i Sani Hanga, wanda shi ne kaɗai Sanatan jam’iyyar NDC, a gidansa da ke Abuja a daren ranar Laraba.
A cewar mai taimaka wa Sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Umar Saminu Mai-Adashi, ganawar ta gudana cikin lumana, inda ɓangarorin biyu suka tattauna kan muhimman batutuwan siyasa da ci gaban Najeriya.
Ziyarar ta sa an fara hasashen cewa Sanata Hanga na shirin ficewa daga jam’iyyar NDC zuwa APC.
Wannan na zuwa ne bayan da Hanga ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda yadda ta ce tsarin Kwankwasiyya ya nuna masa rashin adalci.
Sanata Hanga, wanda tsohon na hannun daman Rabiu Musa Kwankwaso ne, kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, ya ce an cire shi daga jerin ‘yan takarar da jam’iyyar ta amince da su domin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
A farkon wannan makon ne, wata tawagar APC ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kano, Salisu Maje Ahmad Gwangwazo, ta kai masa ziyara tare da neman ya koma jam’iyyar.
Duk da cewa APC ba ta yi masa alƙawarin ba shi tikitin takarar Sanata ba, ta tabbatar masa cewa za a yi masa adalci.
Jam’iyyar APC na ƙoƙarin ƙara ƙarfafa matsayinta a Kano bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar a baya-bayan nan.
Sanata Hanga ya bayyana goyon bayansa ga matakin da gwamnan ya ɗauka.
Ko da yake Sanata Hanga bai sanar da ficewarsa daga NDC a hukumance ba.
Amma ganawarsa da Shugaban APC na Ƙasa ta ƙara ƙarfafa hasashen cewa zai iya komawa jam’iyyar mai mulki nan ba da daɗewa ba.
A baya an bai wa Nasiru Yusuf Gawuna tikitin kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, yayin da aka bai wa Mustapha Rabiu Kwankwaso, ɗan Rabiu Musa Kwankwaso, tikitin Mataimakin Gwamna da ake hasashen za a bai wa Sanata Hanga.
