<span></span>
Shugaban Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato, Honarabul Isa Salihu Kalenjeni, ya yi murabus daga muƙaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki a jihar.
Kalenjeni, ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar APC tare da ajiye muƙaminsa na Shugaban Ƙaramar Hukumar a ranar Talata, 7 ga watan Yuli, 2026.
Ya nemi gafarar al’ummar Tangaza kan duk wani kuskure da ya aikata a lokacin da yake jagorantar Ƙaramar Hukumar, inda ya yi musu fatan alheri.
“Ni ne Isah Salihu Bashar Kalenjeni, zaɓaɓɓen Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza. Ina sanar da ficewata daga jam’iyyar APC, sannan yau na ajiye muƙamina na Shugaban Ƙaramar Hukumar,” in ji shi.
Sai dai wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa ana zargin tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar na shirin komawa wata jam’iyya.
Wasu na ganin jam’iyyar ADC zai koma, lamarin da ake ganin na iya kasancewa dalilin matakin da ya ɗauka.
