Sin Ta Yi Watsi Da Ikirarin Philippine Kan Tekun Kudancinta
Kasar Sin ta sake nanata cewa ikirarin da Philippines ke yi game da tekun kudancinta ba shi da wani asali daga tarihi ko dokokin shari’a, kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin da kuma tsarin kasa da kasa, kamar yadda aka bayyana a wani rahoto mai taken “Suka Kan Tarihi da Dokokin Shari’a Game da Ikirarin Philippines a Tekun Kudancin Sin” wanda ma’aikatar albarkatun kasa ta kasar Sin ta fitar a yau Laraba.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar zaman dar-dar sakamakon abubuwan da Philippines da Japan ke aikatawa kwanan nan, da kuma bayan cika shekaru 10 da kin amincewar Sin da hukuncin sulhu da aka yi wanda Manila ke ci gaba da kafa hujja a kai domin karfafa ikirarinta na teku.
Duk da cewa Sin ta riga ta gabatar da shaidar ikon mallakar yankin kasarta da kuma watsi da ikirarin Philippines a wasu takardu na hukuma a baya, an bayyana sabuwar takardar da aka fitar a matsayin cikakkiyar tantancewa ta farko game da sahihancin ikirarin Manila a tekun kudancin Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
