<span></span>
Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), sun daƙile yunƙurin shigar wasu ’yan ta’adda da ake zargin ’yan ta’addar ISWAP ne na shiga wasu sassan birnin Maiduguri da yankin Buratai na Jihar Borno.
Wanda hakan ya tilasta wa ’yan ta’addan ja da baya bayan wani gagarumin gumurzu da aka gudanar.
Hare-haren sun faru ne tsakanin ƙarfe 12:20 na tsakar dare zuwa 2:30 na dare, zuwa wayewar garin yau Juma’a, lokacin da ’yan ta’addan suka ci gaba da zuwa Muna Garage, yankin Shuwari da yankin Ajilari Cross a wani yunƙuri na neman shiga birnin Maiduguri.
Majiyoyin sojin rundunar OPHK sun tabbatar da cewa sojojin tare da goyon bayan ingantaccen tsarin sintiri da kai ɗauki na gaggawa, sun gano motsin ’yan ta’addan kuma suka yi musu luguden wuta daga wurare daban-daban, lamarin da ya daƙile kai harin da aka shirya kafin ’yan ta’addan su shiga birnin.
Majiyoyin sun ce ’yan ta’addan, waɗanda suka gamu da martanin gaggawa na sojojin, sun yi watsi da barazanar ta su yadda suka tsere cikin ruɗani.
Wani mazaunin garin Maiduguri da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, “Alal haƙiƙa jiya ba su samu damar yin barci ba musamman su da ke zaune a unguwar Ajilari sakamakon irin ƙara da dirin bindigogi da suka riƙa ji tun wajen ƙarfe 12.30 na dare wadda su suna tsammani ma waɗannan ‘yan ta’addan sun samu shigowa cikin garin na Maiduguri ta ko’ina amma cikin ikon Allah zuwa wajen ƙarfe 3.00 na dare suka ji lamarin ya lafa, amma dai ba su samu damar runtsawa ba har gari ya waye.”
A cikin ayyukan da suka shafi haka, sojoji sun kuma daƙile wani yunƙurin kutsa kai da ’yan ta’addan suka yi a Miringa da Dutsen Kura a yankin Buratai na Jihar Borno.
A lokacin da ake bin ’yan ta’addan da suka gudu a Miringa, wata motar kare na’urorin yaƙi da nakiyoyi (MRAP) ta kunna na’urar fashewa (IED). Duk da haka, ba a sami asarar rai a tsakanin sojojin ba kuma yanayin aikin ya kasance daidai.
Majiyoyin tsaro sun ce ana ci gaba da ayyukan share fage da binciken ƙwaƙwaf a yankunan da abin ya shafa don gano ’yan ta’addan da suka gudu, don kuma hana duk wata barazana ga al’ummomin da ke kusa.
