<span></span>
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wata mota da ke ɗauke da tarin miyagun ƙwayoyi a kan titin Legas zuwa Calabar bayan samun sahihan bayanan sirri daga wata majiya.
Rundunar ta ce an gudanar da aikin ne a ranar 9 ga Yulin 2026, inda aka kama direban motar tare da ƙwace kayan da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.
Binciken farko ya nuna cewa ana safarar miyagun ƙwayoyin ne zuwa yankin Berger da ke Jihar Legas, sai dai wanda ake zargin ya kasa bayyana masu kayan ko kuma mutumin da za a kai wa su.
Bayan kammala matakan farko na bincike, rundunar ta miƙa wanda ake zargin tare da miyagun ƙwayoyin ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Legas domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
A halin da ake ciki, Babban Kwamandan Runduna ta 81, Manjo Janar Adebayo Babalola, ya buƙaci dakarun rundunar da su ƙara zage damtse wajen yaƙi da masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran masu aikata laifuka a yankin da suke kula da shi.
