<span></span>
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Wakilai ƙudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya domin bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandansu.
Gwamnatin Tarayya ta ce ƙudirin na da nufin ƙarfafa tsarin tsaro a ƙasar nan tare da bai wa gwamnatocin jihohi damar taka rawar gani wajen tunkarar matsalolin rashin tsaro, musamman hare-haren ’yan bindiga, garkuwa da mutane da rikice-rikicen al’umma.
Idan har Majalisar Tarayya ta amince da ƙudirin, sannan mafi yawan majalisun jihohi suka tabbatar da shi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, jihohi za su samu ikon kafa rundunonin ’yan sandansu, tare da tsara yadda za su gudanar da ayyukansu bisa tanadin dokar da za a kafa.
Batun kafa ’yan sandan jihohi ya daɗe yana jawo muhawara a Najeriya, inda masu goyon bayansa ke ganin zai taimaka wajen inganta tsaro ta hanyar kusantar jami’an tsaro da al’umma, yayin da masu adawa da shi ke nuna fargabar yiwuwar amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa ko tauye haƙƙin ɗan ƙasa.
