<span></span>
Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe (SSG) kuma Shugaban Kwamitin Dattawan PDP, Alhaji Bala Muhammad Magaji, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.
Magaji, wanda shi ne Magajin Garin Gombe, ya gana da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a Fadar Gwamnatin Jihar Gombe.
Taron ya samu halartar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, wanda suka tarbe shi zuwa APC.
Ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda irin salon shugabancin Gwamna Inuwa Yahaya da kuma ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ta aiwatar a jihar.
Magaji, ya sanar da ficewarsa daga PDP cikin wasiƙar da ya aike wa shugaban jam’iyyar a mazaɓarsa.
Ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi na yin aiki tsawon shekaru, amma ya ce abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar ba su dace da aƙidun siyasarsa ba.
Ya kuma yi murabus daga muƙaminsa na Shugaban Kwamitin Dattawan PDP nan take.
Ana ganin komawar Bala Magaji APC babbar nasara, musamman yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jam’iyyar PDP a jihar ba ta fitar da wata sanarwa kan ficewarsa ba.
