<span></span>
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta kama wani mutum, mai suna Amos Paul, bisa zargin ƙone al’aurar ’yarsa mai shekara 10 da dutsen guga saboda tana fitsarin kwance.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Unaun da ke Upenme, a Ƙaramar Hukumar Owo ta Jihar Ondo.
An kama mutumin ne bayan an kai wa ’yan sanda rahoton faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ya ce yarinyar ta samu munanan raunuka, kuma an garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da ke Owo, inda ta ke karɓar magani.
Jimoh, ya ce jami’an ‘yan sanda na yankin Owo sun yi gaggawar zuwa wajen da lamarin ya faru tare da kama wanda ake zargin.
Ya ce an miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken laifukan da suka shafi mata da yara (Gender Unit) domin ci gaba da bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ondo, CP Felix Ohagwu, ya yi Allah-wadai da lamarin.
Ya ce rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da kare yara da sauran mutane masu rauni daga cin zarafi, tashin hankali da amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya kuma tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.
Kwamishinan ya buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani cin zarafin yara, rikici zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike a kan lamarin, yayin da wanda ake zargin ke tsare a hannun ‘yan sanda.
