<span></span>
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya buƙaci masu hannu da shuni da su riƙa tallafa wa iyalan da ba su da hali wajen bai wa ’ya’yansu damar samun ilimi.
Sarkin ya yi wannan kira ne a wajen bikin yaye ɗaliban Makarantar UMRABS da ke Tudun Jukun a Ƙaramar Hukumar Zariya.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar iyaye da malamai wajen tabbatar da tarbiyya da ingantaccen ilimi ga yara, tare da yaba wa ɗaliban bisa bajintar da suka nuna da kuma malamai saboda jajircewarsu wajen koyarwa.
Sarkin ya yaba wa makarantar kan yadda take tafiyar da harkokin ilimi, musamman haɗa karatun zamani da na addini.
A nasa jawabin, Daraktan makarantar, Dokta Isa Saidu, ya gode wa Sarkin Zazzau da tawagarsa bisa halartar bikin, yana mai cewa hakan babban abin ƙarfafawa ne ga makarantar.
Dokta Isa ya ce tarihi ba zai manta da wannan babban karamci da Sarkin ya yi masu ba har duniya ta naɗe.
Ya kuma tunatar da iyaye muhimmancin biyan kuɗin makaranta a kan kari da kiyaye ƙa’idojin da hukumar makaranta ta tanda, tare da bayyana cewa UMRABS ba ta tatsar iyaye kuɗaɗen da ba su dace ba a lokutan bikin yaye ɗalibai.

