<span></span>
’Yan bindiga sun kashe Hakimin Kulodo da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a Jihar Sakkwato, Alhaji Abubakar Tudu, da babban ɗansa tare da wasu mutum biyar a hare-haren da suka kai ƙauyukan Kulodo da Kwance.
Harin ya faru ne a ranar Juma’a yayin da mazauna yankin suke tsaka da sallar La’asar.
Wata majiyar tsaro ta ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyukan a kan babura, inda suka riƙa harbe-harbe, sannan suka kwashe dabbobi masu yawa zuwa cikin dajin Jihar Zamfara.
“Sun shigo ƙauyukan da yawa, kuma da isowarsu suka fara harbe-harbe.
“Sun kashe hakimin ƙauyen, babban ɗansa da wasu mutane huɗu kafin daga bisani su wuce ƙauyen Kwance inda suka kashe wani mutum guda ɗaya,” in ji majiyar.
Majiyar ta ce ba su yi awon gaba da kowa ba, amma sun tilasta wa makiyaya kora shanun da suka sace.
Ta kuma ce mata da yara da dama sun tsere daga ƙauyukan saboda fargabar hare-haren.
“Lamarin ya yi muni matuƙa. Kusan duk mata da yaran yankunan nan sun tsere, sai kaɗan daga cikin maza ne suka rage a ƙauyukan,” in ji majiyar.
Wannan harin ya faru ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan da wasu ’yan bindiga suka kashe Babban Limamin ƙauyen Kallejo da wasu mutum biyu yayin wani hari da suka kai Ƙaramar Hukumar Bodinga.
A sakamakon hare-haren, wasu fusatattun matasa sun tare babbar hanyar Sakkwato zuwa Jega a ranar Juma’a domin nuna rashin amincewarsu da yadda hare-haren ’yan bindiga ke ƙaruwa a yankin.
Rahotanni sun ce matasan sun kunna wuta a kan hanyar tare da dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na sa’o’i kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.
Wani mazaunin yankin ya ce masu zanga-zangar sun hana Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Tukur Bala Bodinga, wucewa tare da lalata gilashin motarsa.
Daga baya jami’an tsaro sun kwantar da tarzomar, yayin da jami’an gwamnatin jihar suka ziyarci yankunan da abin ya shafa domin jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
