<span></span>
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da ƙwato wata mota da aka sace da kuma wasu makamai da ake zargin ana amfani da su wajen fasa gidajen jama’a.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an samu nasarar ne sakamakon tattara bayanan sirri da jami’an ’yan sanda ke yi a sassan jihar.
Haka kuma a wani samame, jami’an sun kama Micah Nuhu bisa zargin yi wa wata mata mai suna Mama Kingsley Joseph fashi da makami.
Ana zargin ya doka mata taɓarya sannan ya ƙwace mata jakarta.
An ƙwato jakar, yayin da aka kai matar asibiti domin kula da lafiyarta.
Rundunar ta ce ana ci gaba da neman wani da ake zargi mai suna Mubarak, wanda ya tsere bayan harin.
An kuma miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin ci gaba da bincike.
A wani samame kuma, ’yan sanda sun kama Nasiru Aminu da Jamiu Muhammad a yankin Tumfure da ke Ƙaramar Hukumar Akko.
Sun ƙwato makullan buɗe ƙofofi guda 39 da kayayyaki, waɗanda ake zargin ana amfani da su wajen fasa gidajen jama’a.
Haka kuma, jami’an sun ƙwato wata mota ƙirar Toyota Yaris da aka sace bayan wasu da ake zargi sun kai wa mai motar hari da wuƙa kafin su tsere da ita.
An gano motar a kusa da Barikin Sojoji da ke Gombe, yayin da aka kai mai motar asibiti domin kula da shi.
Rundunar ta ce tana ci gaba bincike domin cafke sauran waɗanda ke da hannu a laifukan.
Haka kuma ta yi kira ga jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin yaƙi da masu aikata laifuka.
