<span></span>
Rundunar ’Yan sandan Najeriya reshen Jihar Sakkwato ta ce ta daƙile wani hari da ake zargin ’yan bindiga sun kai ƙauyen Daraye da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko, inda ta kashe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin tare da ƙwato bindigar AK-47 da harsasai.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar, inda ya ce nasarar na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin da rundunar ke yi na yaƙi da ’yan bindiga da sauran barazanar tsaro a faɗin jihar.
A cewar sanarwar, an gudanar da aikin ne bayan rundunar ta samu kiran gaggawa wanda ya ankarar da su cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne masu ɗauke da muggan makamai sun mamaye ƙauyen Daraye.
Bayan samun rahoton, jami’an Sashen Yaƙi da Masu Garkuwa da Mutane, da Sashen Daƙile Laifuka a Ƙauyuka (VCRU), tare da sauran ƙungiyoyin musamman, sun garzaya yankin domin kai ɗauki ga jami’an da ke Hedikwatar ’Yansandan Wamakko.
Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun yi musayar wuta mai tsanani da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga daban-daban.
A yayin sintiri da bincike da aka ci gaba da yi a yankin, jami’an sun kashe mutum ɗaya da ake zargin ɗan bindiga ne, sannan suka ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya da ƙwanson harsasai ɗauke da harsasai masu rai guda 28 na nau’in 7.62mm.
Rundunar ta ce an ƙara yawan sintirin tsaro a yankin, tare da sanya ofisoshin ’yansanda da ke maƙwabtan yankuna cikin shirin ko-ta-kwana domin cafke waɗanda suka tsere, musamman idan suka nemi kulawar lafiya sakamakon raunukan da suka samu.
