<span></span>
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da aikata fashi da makami, tare da ƙwato wayoyi guda uku ƙirar iPad da ake zargin sun sato a Ƙaramar Hukumar Fune.
Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce an kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda da ke Damagum, bayan wasu mahara sun kai wa manoma biyu hari a gonarsu da ke ƙauyen Lawan Kalam, cikin gundumar Ngelzarma.
Rahotanni sun nuna cewa da misalin ƙarfe 2:45 na daren ranar 11 ga watan Yuli, maharan ɗauke da adda, wuƙaƙe da sanduna suka shiga ɗakin manoman yayin da suke barci.
Sun yi musu raunuka sannan suka sace wayoyinsu ƙirar iPad guda uku da kuma agogon hannu.
Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun kai ɗauki tare da bin sahun waɗanda ake zargin.
Bincike ya kai ga cafke Idriss Gako da Babangida Abdulrahman, dukkaninsu mazauna ƙauyen Lantewa.
‘Yan sanda sun ce sun ƙwato wayoyin ƙirar iPad guda uku daga hannun waɗanda ake zargin.
A halin yanzu suna tsare a hannun ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike domin gano ko suna da hannu a wasu fashi da makami a yankin.
Rundunar ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
