<span></span>
Fursunoni 61 da ke zaman hukunci a Gidan Gyaran Hali mai Matsakaicin Tsaro (Medium Security Custodial Centre – MSCC) da ke Kurmawa a Jihar Kano sun kammala haddar Alƙur’ani Mai Tsarki.
Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya ta bayyana matakin a matsayin babban ci gaba a shirinta na gyaran hali da sake dawo da fursunoni cikin al’umma.
Waɗanda suka kammala haddar sun haɗa da maza 55 da mata shida, waɗanda suka jajirce kuma suka yi ƙwazo da haƙuri a tsawon lokacin gudanar da shirin.
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce da dama daga cikin fursunonin ba su da cikakken ilimin karatun Alƙur’ani kafin shigarsu gidan gyaran hali.
Sai dai ta hanyar tarbiyya, jajircewa da kuma ingantaccen koyarwar addini, sun sami damar kammala hardar Alƙur’ani Mai Tsarki.
Ya ce wannan nasara na nuna irin tasirin shirye-shiryen gyaran hali na addini da hukumar ke aiwatarwa, tare da tabbatar da aniyarta na gyarawa, horaswa da sake shigar da fursunoni cikin al’umma kamar yadda Dokar Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya ta shekarar 2019 ta tanada.
A cewarsa, domin karrama waɗanda suka kammala hardar, hukumar tare da haɗin gwiwar wata ƙungiya mai zaman kanta, sun ba kowannensu tallafin jin daɗi da ya haɗa da sabbin kaya, katifa, bargo da kuma tallafin kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da rayuwa ta gari da kuma sauƙaƙa musu komawa cikin al’umma bayan kammala zaman hukuncinsu.
Kofar Nasarawa ya ƙara da cewa Kwanturolan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yaba wa Babban Kwanturola Janar na Hukumar na Ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa ci gaba da ba da goyon baya ga shirye-shiryen ilimi, koyon sana’o’i da tarbiyya a gidajen gyaran hali a faɗin ƙasar nan.
Lakpene ya ce irin waɗannan shirye-shiryen na taimaka wa fursunoni wajen samun ilimi, ƙwarewa da kyawawan ɗabi’u da za su ba su damar zama ’yan ƙasa nagari masu amfani ga al’umma bayan sun samu ’yanci.
Shi ma wani masani a fannin ilimi, Farfesa Aliyu Haruna, ya yaba wa hukumar bisa ƙoƙarin da take yi na sauya rayuwar fursunoni ta hanyar shirye-shiryen gyaran hali masu ma’ana, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen mayar da su mutane nagari masu bin doka da oda.
A nata jawabin, Shugabar Kwamitin Bai wa Fursunoni Afuwa ta Jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na inganta walwalar fursunoni, tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ci gaba da tallafa wa fursunonin da ke gidajen gyaran hali a jihar.
A nasa jawabin, Limamin gidan gyaran hali, DSC Mohd Alkanawy, tare da Babban Limami, Imam Nasiru Abdu, sun yi wa waɗanda suka kammala hardar nasiha da su ci gaba da riƙo da ladabi, kyawawan ɗabi’u da ci gaban addini da suka samu yayin shirin.
Hakimin Kawaji kuma Ɗan Ruwatan Kano, Alhaji Ibrahim Ado Bayero, ne ya gabatar da takardun shaidar kammala hardar ga fursunoni 61 da suka kammala shirin.







