<span></span>
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar ƙasa biyu da suka afku a Venezuela ya ƙaru zuwa 4,490, yayin da sama da 16,740 suka jikkata, kamar yadda gwamnati ta sanar.
Girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.2 da 7.5 ta afku ne a ranar 24 ga Yuni, inda ta lalata gine-gine da dama a birnin Caracas da Jihar La Guaira.
Gwamnati ta ce mutane 19,583 da suka rasa matsugunansu na ci gaba da zama a sansanonin wucin gadi da aka kafa a filayen wasa da sauran wurare.
Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar, Jorge Rodriguez, ya ce gwamnati za ta fara bai wa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa gidajen da ake kammalawa, tare da ware filaye sama da 40 domin gina sababbin gidaje.
A halin da ake ciki, Rasha ta aika da kayan agaji zuwa Venezuela, yayin da Amurka ta sanar da kai kayan agaji 100,000 ga al’ummomin da bala’in ya shafa.
