<span></span>
Majalisar Dattawa, ta bai wa iyalan mutane biyar da suka rasa rayukansu wajen ceto ɗaliban makaranta da aka sace a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo, tallafin Naira miliyan 50.
Majalisar ta ce kowanne daga cikin iyalan mamatan zai karɓi Naira miliyan 10.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce an bayar da tallafin ne domin taimaka wa iyalan da yaran da mamatan suka bari.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da sojoji biyu, ɗan sanda ɗaya da malamai biyu.
Jami’an tsaro sun samu nasarar ceto ɗalibai 39 da malamai bakwai da aka sace.
Majalisar ta kuma yaba wa jami’an tsaro da malamai bisa jarumta da sadaukarwar da suka nuna, inda ta ce hakan ya taimaka wajen ceto rayukan ɗalibai da dama.
’Yan majalisar sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara inganta ayyukan tsaro, bunƙasa tattara bayanan sirri da kuma samar da ƙarin tallafi ga jami’an tsaro domin daƙile hare-haren ’yan ta’adda a faɗin ƙasar.
