<span></span>
Sojoji biyu na rundunar dakarun tsaron Afirka ta Kudu (SANDF) sun mutu bayan da suka rufta cikin wani tsohon ramin haƙar ma’adinai a Johannesburg yayin wani samame da suke kai wa masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kuma shi ne karo na farko da aka samu asarar rayukan jami’an tsaro tun bayan da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya tura sojoji a watan Maris domin ƙarfafa ayyukan yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamnatin ƙasar ta tura kusan sojoji 2,200 zuwa sassa daban-daban na ƙasar domin taimaka wa ’yan sanda wajen daƙile ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka ƙara yawaita a baya-bayan nan.
Kakakin rundunar ’yan sandan ƙasar, Athlenda Mathe, ta ce hatsarin ya faru ne a wani tsohon wurin haƙar zinare da aka yi watsi da shi a yammacin Johannesburg, yayin da sojojin ke bin waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda aka fi sani da “zama zamas.”
Ta ce sojojin sun faɗa ne cikin wani rami mai zurfi da aka daina amfani da shi.
Rundunar Tsaron Ƙasa ta Afirka ta Kudu (SANDF) ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa hatsarin ya auku da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, yayin da ake ci gaba da tattance bayanai kan waɗanda suka rasu.
Muƙaddashin Ministan ’Yan Sandan ƙasar, Firoz Cachalia, ya bayyana rasuwar sojojin a matsayin babban rashi ga hukumomin tsaro da kuma ƙasar baki ɗaya.
Masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda galibinsu ke fitowa daga ƙasashe maƙwabta irin su Mozambique, Zimbabwe da Lesotho, sun mamaye tsofaffin wuraren haƙar ma’adinai da ke kewaye da Johannesburg da sauran garuruwan da ke maƙwabtaka da su.
