<span></span>
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙasarsa ta ƙulla tsakaninta da Iran ta rushe bayan sabbin hare-haren da ɓangarorin biyu suka kai wa juna.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a gefen taron ƙasashen NATO da aka gudanar a Ankara ranar Laraba.
Ya ƙara da cewa ba ya son ci gaba da mu’amala da Iran, yana mai bayyana tattaunawa da ƙasar a matsayin “ɓata lokaci.”
Trump ya kuma yi kalamai masu zafi kan shugabannin Iran, yana mai cewa ba ya ganin wata fa’ida a ci gaba da yin hulɗa da su.
Kalaman na Trump na zuwa ne bayan Iran da Amurka sun yi musayar hare-hare tare da zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a baya, lamarin da ya sake ƙara tayar da hankalin rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Aminiya ta ruwaito cewa dakarun juyin juya hali na Iran sun sanar da kai hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Kuwait, a matsayin martani kan harin da Washington ta kai mata, bayan zarginta da farmakan jiragen ruwan kasuwanci a Mashigar Hormuz.
Tun farko Amurka ce ta sanar da sake ƙaddamar da sabon farmakin kan Iran, sakamakon hare-hare da ake zargin Iran ɗin ta kai kan jiragen ruwa a mashigin ruwa na Hormuz, abin da ya sa Tehran ta mayar da martani mai zafi wajen farmakar sansanonin Amurka a yankin Gulf.
Wani masanin harkokin tsaro a Jami’ar King’s College da ke Landan, Andreas Krieg, ya ce Iran na ci gaba da dagewa kan buƙatarta ta karɓar harajin amfani da Mashigar Hormuz, duk da cewa Amurka ta ce ba za ta amince da hakan ba.
“Yanzu ana cikin wani yanayi mai matuƙar muhimmanci inda ake neman wasu hanyoyin da za su maye gurbin tsarin kuɗin fito da Iran ke son ƙaƙaba wa jiragen ruwa,” in ji Krieg.
Ya ƙara da cewa, “Iran na aika saƙo ne ƙarara cewa ba za ta amince da wata mafita da ta saɓa wa wannan matsayi ba.”
