<span></span>
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya ce yana sa ran ƙaddamar da aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK) a watan Satumban bana.
Mai magana da yawun NNPCL, Andy Odeh, ya ce aikin ya kai kashi 98 cikin 100, inda aka kammala shimfiɗa bututun iskar gas daga Ajaokuta da ke Jihar Kogi zuwa Kano.
Sai dai kamfanin ya bayyana cewa a halin yanzu an mayar da hankali ne kan kammala muhimman ayyukan na kan tudu, waɗanda za su taimaka wajen karɓa da kuma sa ido kan zirga-zirgar iskar gas, lamarin da ke nuna har yanzu ba a ayyana takamaiman ranar fara aiki da bututun ba.
Binciken Weekend Trust ya nuna cewa har yanzu ba a fara gina mafi yawan tashoshin karɓar iskar gas da cibiyoyin ajiyarsa da za su kasance a kan hanyar bututun ba, sai dai a yankin Ajaokuta.
Majiyoyi sun ce a Ajaokuta wasu masu zuba jari masu zaman kansu sun fara gina tashoshin da za su rarraba iskar gas zuwa sassan Arewacin Najeriya, kasancewar ita ce hanya mafi sauƙi ta isar da iskar da za ta riƙa fitowa ta bututun.
Sun ce an zaɓi wannan tsari ne domin sauƙaƙa samar da iskar gas yayin da ake ci gaba da gina sauran muhimman kayayyakin aikin.
Sai dai masana sun kuma yi gargaɗin cewa ci gaba da jinkirin aikin na iya jawo wa martabar Najeriya naƙasu, ganin cewa bututun AKK na da muhimmiyar rawa wajen aiwatar da aikin bututun iskar gas a faɗin yankin Saharan, wanda ake sa ran zai bai wa Najeriya damar fitar da iskar gas zuwa Turai.
An ƙaddamar da aikin ne a shekarar 2020, kuma duk da cewar an shafe kusan shekara shida ana gudanar da shi, har yanzu ba a kammala shi ba duk da alƙawuran da aka yi a baya na fara amfani da shi.
