<span></span>
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hukumar za ta gudanar da sahihin zaɓe a shekarar 2027.
Amupitan ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin da ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, a gidansa da ke Minna, Jihar Neja.
Farfesa Amupitan ya ce hukumar za ta tabbatar da an ƙirga duk wata ƙuri’ar da aka kaɗa bisa tanadin doka.
Kazalika, ya ce INEC za ta ci gaba da kare mutunci da sahihancin tsarin zaɓe, duk da sa ido da kuma mabambantan ra’ayoyin da ake faɗi kan shugabancin hukumar daga sassa daban-daban na ƙasar.

