An kaddamar da Kimi K3, wani samfurin kirkirrarriyar basira ta AI da kamfanin Moonshot AI na kasar Sin ya samar, a ranar Juma’ar da ta gabata, wanda ya zama wata sabuwar nasara a fannin raya AI mai budadden tsari. A cewar kamfanin Moonshot AI, Kimi K3 mai kididdigar koyo triliyan 2.8, ya zama samufurin AI mai budadden tsari mafi girma a duniya. Haka kuma, samfurin ya nuna matukar kwazo a fannonin nazari da dama, inda ya zama cikin tsare-tsaren AI da ke kan gaba a duniya. Sa’o’i kalilan bayan fitar da shi, Kimi K3 ya kai matsayi na 1 cikin jerin AI mafiya inganci na Arena Rankings, inda ta zama fasahar AI ta kasar Sin ta farko da ta kai matsayi na 1 a dandalin mai tasiri. Masu nazari a masana’antar AI sun ce wannan nasara ba ci gaban fasaha kadai take nunawa ba, har da karuwar rawar da bayyana komai ke takawa da hadin gwiwa da samar da muhallin raya makomar fasahar AI a duniya. (Fa’iza Mustapha)
Manyan kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru guda biyu sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su,...
Mutum shida sun rasa rayukansu, yayin da wasu 32 suka jikkata bayan wata girgizar...
Mutum shida sun rasu, yayin da aka ceto mutum 15 da ransu bayan wani...
ICPC ta shigar da tuhume-tuhume guda huɗu a gaban kotu kan Farfesa Bello Abubakar, babban likitan da...
Ƙungiyar Hamas ta sanar da naɗa Khalil al-Hayya a matsayin sabon shugabanta, wanda ya...
Mutum shida sun rasu, yayin da wasu huɗu suka jikkata bayan tsawa ta faɗa...
Ana fargabar cewa kimanin mutum huɗu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da...
A ranar Lahadi 19 ga watan Yuli na shekarar 2026 aka buga wasan karshe na gasar kofin...
Dakarun Operation Hadin Kai sun kama wani ɗan ƙasar Sudan mai shekaru 32, Musa Fashir, da wata...
